Wasanni

Real Madrid na tattaunawa da Luka Modric kan sabunta kwantiragin shi da kolub ɗin

Luka Modric ya kusa rattaba hannu kan sabon kwantaragi na shekara daya da Real Madrid, duk da cewa bangarorin biyu ba su cimma cikakkiyar yarjejeniya ba tukuna.

Dan wasan na Croatia yana da shekaru 36, amma ya kasance muhimmin bangare na tawagar Carlo Ancelotti kuma ya yi rawar gani a wasan da Real ta doke Paris Saint-Germain da ci 3-1 a gasar zakarun Turai a cikin mako.

Ya rattaba hannu kan sabon tsawaita wa’adin shi kafin a fara kakar wasa ta bana amma ana cigaba da tattaunawa kan wata yarjejeniya da za ta tsawaita zaman shi a Bernabeu.

Advertisement

Marca  ta rahoto cewa yayin da aka cimma yarjejeniya ta baki a farkon wannan shekarar, ba a kammala tattaunawa ba kuma wasu manyan kungiyoyin Turai suna ci gaba da sha’awar daukar tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham.

Advertisement