Wasanni

Rasha zata kai FIFA da UEFA kara a kotu kan dakatar da ita daga wasan kwallon kafa

Rasha na shirin daukaka kara kan haramcin kwallon kafa da hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, da hukumar kwallon kafar Turai, UEFA, suka kakabawa kasar.

Ƴan kwanakin kungiyoyin kwallon kafar biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a ranar Litinin, tare da dakatar da kungiyoyin kwallon kafa na kasar – kungiyoyi da na kasa – har zuwa wani lokaci.

Matakin dai ya biyo bayan harin da kasar Rasha ta kai makwabciyar ta Ukraine a ranar Alhamis din karshen watan Fabrairun 2032, yayin da ake cigaba da gwabza fada tsakanin kasashen biyu.

Advertisement

Sai dai Hukumar Kwallon Kafa ta Rasha, a ranar Alhamis, ta ce za ta garzaya Kotun Hukunta Wasanni (CAS) don daukaka kara kan hukuncin da FIFA da UEFA suka yanke.

Kungiyar ta ce za ta shigar da kara guda daya a kan kungiyoyin biyu, inda ta bukaci a ba wa yan wasan kasar Rasha maza da mata damar shiga gasar.

Advertisement