Kasuwanci

Rasha Vs Ukraine: Biden ya hana Amurka shigo da mai da iskar gas na Rasha

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da cewa Amurka zata hana shigo da man fetur da iskar gas daga kasar Rasha, a wani mataki na matsawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin lamba kan ya kawo karshen yakin Ukraine.

Da yake magana a fadar White House da safiyar Talata, Biden yace matakin ya shafi “babban jigon tattalin arzikin Rasha”.

“Muna hana duk wani shigo da mai da iskar gas da makamashi na Rasha. Hakan na nufin ba za a sake karbuwar man Rasha a tashoshin jiragen ruwa na Amurka ba kuma jama’ar Amurka za su sake yin wani mummunan rauni ga injin yakin Putin,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Advertisement

Masu fafutukar kare hakkin bil adama da shugabannin Ukraine sun yi kira ga Amurka da kawayenta na Turai da su kakabawa bangaren mai da iskar gas na Rasha takunkumi, sakamakon mamayar da kasar ta yi wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, wanda ya lalata manyan biranen kasar tare da tilastawa mutane miliyan biyu barin kasar.

Kasashen yammacin duniya, musamman kasashen Turai da ke dogaro da mai da iskar gas na Rasha don samun kaso mai tsoka na bukatun makamashinsu, sun yi jinkiri a cikin fargabar hana su katse su daga kayayyakin da ake bukata da kuma sanya farashin tashin gwauron zabi.

Advertisement