Tsaro

Rasha ta yi asarar fiye da sojoji 11,000, jirage 114, tankokin yaki 290 da sauran su – Ukraine

An ba da rahoton cewa sojojin Rasha sun yi asarar sojoji fiye da 11,000 tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu, 2020.

A cewar wata majiya, sojojin sun yi asarar sama da dakaru 11,000, da jiragen sama 46, da jirage masu saukar ungulu 68, da motocin sulke 999, da kuma tankokin yaki 290 a yakin da ake yi a Ukraine.

An yi zargin cewa hukumomin Ukraine ne suka bayyana hasarar rayuka da asarar da sojojin Rasha suka yi a yayin da Rasha ke cigaba da gudanar da cikakken aikin soji a duk fadin kasar ta Ukraine a cewar Vladimir Putin.

Advertisement

Haka zalika, fararen hula da dama sun jikkata tare da rasa matsugunan su sakamakon rikicin Rasha da Ukraine da ya barke a yan makonnin da suka gabata ba tare da la’akari da tofin Allah tsine da rashin amincewa da kungiyoyin kasa da kasa suka yi ba.

Kasashe da dama da suka hada da Najeriya da Indiya da Afirka ta Kudu da Ghana da kuma ‘yan kasar Ukraine sun tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta domin neman mafaka a ci gaba da aiyukan soji a garuruwan Ukraine da sojojin Rasha ke yi.

Menene ra’ayinku game da wannan ci gaban bayan asarar da sojojin Rasha suka yi?

Advertisement