Labarai

Rasha Ta Kashe Sojojin Yukiren 945 A Wani Ƙazamin Farmaki

Rundunar sojin Rasha ta ce dakarunta na ci gaba da dakile harin da dakarun Ukraine suka kai musu.

Har ila yau, ta yi ikirarin cewa dakarun Ukraine sun yi asarar sojoji 945 da kuma motocin sulke 102, ciki har da tankokin yaki 12, a farmakin da suka kai kawo a Kursk.

Al Jazeera ta gagara tabbatar da alkaluman na Moscow.

Rundunar sojin Rasha ta kuma bayar da rahoton fafatawa a wajen yammacin Sudzha inda ta ce an kuma gwabza fada a kusa da kauyukan da ke kusa da kan iyakar ta da Yukiren.