Wasanni

Qatar 2022: Bugun Fenaretin Bale Ya Ceci Wales A Wasan Su Da Amurka

Gareth Bale ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda ya taimaka wa Wales ta dawo daga baya inda suka tashi kunnen doki 1-1 da Amurka a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2022.

Timothy Weah ne ya fara zura kwallo a ragar Amurka ta hannun Christian Pulisic a minti na 36 da fara wasa kafin daga bisani Wales ta samu bugun fanariti a minti na 82.

Tim Ream yayi taɓa kwallon a cikin akwatin, sannan Bale ya ci bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda ya kai matakin wasan.

Advertisement