Wasanni

Qatar 2022: An Yiwa Lionel Messi Alƙawarin Zama Shugaban Kasar Argentina

Tsohon shugaban kasar Argentina, Mauricio Macri, ya dage cewa kyaftin Lionel Messi ne za a zaba a matsayin shugaban kasa idan ya kai La Albiceleste ta lashe gasar cin kofin duniya na FIFA na bana a Qatar.

Tuni dai Argentina ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.

Tawagar Lionel Scaloni ta lallasa Australia da ci 2-1 a zagaye na 16 inda suka samu damar zuwa zagaye na 8 na karshe.

Advertisement

Messi ya zama dan wasan da yafi kowa taka rawar gani a Argentina, inda ya zura kwallaye uku ya kuma taimaka daya ya zuwa yanzu, kuma Macri yayi imanin cewa dan wasan gaba na Paris Saint-Germain zai zama shugaban kasar Argentina idan ya samu nasara a kokarin shi.

“Dukkan mu za mu zabe shi [Messi] a matsayin shugaban kasa, eh (dariya). Abu mafi mahimmanci shi ne cewa ƙungiyar ta ji daɗin kan su, yanayin yana da kyau kuma wannan shine yabo na Scaloni, “Macri ya gaya wa MARCA.

“Ma’aikatan horarwa mutane ne masu lafiya. Abin mamaki a gasar cin kofin duniya shine magoya bayan Argentina.”

Ya kara da cewa, “Leo Messi, wanda ba wai kawai ya fi kowa kyau a duniya ba, amma kashi 80% na mutanen Doha suna son Messi ya zama zakaran duniya.”

Advertisement