Tsaro

Putin ya ce zai kawo mayaka daga yankin gabas ta tsakiya domin hada karfi da karfe a Ukraine

Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa zai kawo mayaka daga yankin gabas ta tsakiya domin hada karfi da karfe a Ukraine.

Advertisement

Vladimir Putin ya bayyana cewa za a karbi sojojin haya daga ko’ina cikin duniya kuma za a kawo su Ukraine tun da kasashen Yamma suna daukar nauyin Ukraine kuma suna bayyanawa jama’a game da hakan.

Yakin Ukraine ya sake daukar wani mataki tun bayan da sojojin Rasha suka tsananta kai hare-hare, da kai hare-hare ta sama, da kuma mamaye garuruwa daban-daban na Ukraine, a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya suka yi kira da a tsagaita wuta a Ukraine.

Advertisement

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayi gargadin cewa duk wata hukuma da ta tsoma baki a cigaba da mamaye kasar Ukraine da suke yi zata shiga cikin rikicin da aka ce yayi sanadiyyar rasa matsuguni da dubban mutane.

Fiye da mutane miliyan daya ne suka tsere daga kasar Ukraine ciki har da ‘yan kasashen Afirka bayan barkewar yakin Rasha da Ukraine wanda ya fara a ranar 24 ga Fabrairu, 2022.

Advertisement