Kasuwanci

POS: Hukumar Birnin Abuja Ta Fara Gangamin Cire Shagunan Masu POS A Kan Hanya

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar babban birnin tarayya FCTA ta haramta ayyukan ma’aikatan kamfanin na Point of Sales (POS) a gefen titi da wuraren da ba su da izini a kan tituna.

Umar Shuaibu, Ko’odinetan Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja (AMMC), ya yi ikirarin cewa an dauki matakin ne domin magance matsalar rashin tsaro da ke biye da su.

Duk da cewa gwamnatin ba ta yi adawa da ayyukan POS a Abuja gaba daya ba, ya yi nuni da cewa gudanar da ayyuka ba tare da tsangwama ba da haifar da matsala ya saba wa ka’idojin muhalli.

Advertisement

Kwamared Ikharo Attah, babban mataimaki na musamman ga ministan babban birnin tarayya Abuja akan sa ido, dubawa, da tabbatar da tsaro ya kara da cewa ministan babban birnin tarayyan ya ki amincewa da mutanen da ke buga ma’aikatan POS dinsu ba bisa ka’ida ba a wuraren da ke kawo barazana ga tsaro.

Yayin da ƙungiyar tilastawa ba za ta damu da masu aiki da ke iyakance ayyukansu a cikin wuraren kasuwanci ba, waɗanda ke haifar da tashin hankali da barazanar tsaro za a cire su.

Ya ce, “Ministan FCT ba ya adawa da kasuwancin POS amma yana yaki da ayyukan da ba su ji ba gani da ke shafar tsaron mazauna yankin.

“Akwai koke-koke da mazauna yankin ke yi cewa bakon mutane na yin amfani da POS ba gaira ba dalili a cikin kofofinsu da titunansu

“Muna goyon bayan kasuwancin POS, amma muna fusata kan ayyukan da ke barazana ga tsaron mutanenmu,” in ji shi.

Advertisement