Siyasa

PDP ta lashe zaben ciyamn na karamar hukumar ‘Kuje’ a Abuja

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a yau Lahadi ta bayyana Suleman Sabo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ciyaman Kuje da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja ranar 12 ga watan Fabrairu.

Advertisement

Sule Magaji jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a karamar hukumar Kuje ne ya sanar da sakamakon zaben da safiyar Lahadi.

Mista Sabo, wanda shi ne shugaban karamar hukumar ya doke wasu yan takara biyar a kowace shiyya 10 na karamar hukumar.

Advertisement

Ya samu kuri’u 13,301 inda ya kayar da babban abokin hamayyar shi, Sarki Hamidu na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 7,694 ya zo na biyu.

A halin da ake ciki, dan takarar shugabancin jam’iyyar Labour Party (LP) Loveday Ajo ya samu kuri’u 79.

The PDP candidate defeated the APC with a total margin of 5,607 votes.

Advertisement