Siyasa

PDP ba kadarar ka ce ba – Obaseki ya mayarwa Wike martani

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya gargadi takwaran shi na jihar Ribas, Nyesom Wike, kan tursasawa da barazana ga ya’yan jam’iyyar PDP da ke bayyana ra’ayoyin su kan harkokin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa dukkan mambobin jam’iyya daya ne.

Advertisement

Obaseki ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga Wike saboda kalaman da yayi ga mataimakin shi (Obaseki), Philip Shaibu, wanda ya koka da yadda shi da magoya bayan shi ke fama da rashin natsuwa a Edo PDP bayan sun sauya sheka a 2019 daga APC zuwa PDP.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun shi, Obaseki ya zargi Wike da rike PDP tamkar kadarar shi ce.

Advertisement

Ya bayyana mamakin shi yadda Wike zai iya kai wa Shaibu hari ba tare da tuntubar shi (Obaseki) a matsayin shi na abokin aikin shi ba kafin ya fito fili.

Sanarwar ta kara da cewa, “Babu wanda ke adawa da muradin shi na tsayawa takarar shugaban kasa, duk da haka, bai kamata a aiwatar da burin shi ta yadda zai kawo cikas a matakai daban-daban, kamar kungiyar gwamnonin PDP da ma daban-daban, sassan jam’iyyar a fadin kasar.

“Yayin da Gwamna Wike yake da ’yancin yin amfani da dukiyarsa yadda ya ga ya dace wajen cimma burinsa, bai kamata ya yi yunkurin kiwo, tsoratarwa, cajole da kuma yi wa wasu barazana ba. Jihar Edo ba za ta iya ba kuma ba za a siya don burin kowa ba.”

Obaseki, yayin da yake wanke Shaibu, ya bayyana irin abubuwan da Wike ya yi wa PDP barazana.

Advertisement