Siyasa

Osun: Oyetola ta lashe mazabar shi a zaben fidda gwani na gwamna a APC

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya doke yan takarar biyu da suka haɗa da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Moshood Adeoti da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yusuf Lasun, a zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a unguwar shi ta Iragbiji a yau Assabar, karamar hukumar Boripe.

Jami’in zaben, Samson Oyebade, wanda ya bayyana sakamakon zaben da aka gudanar a makarantar St. Peters Primary School, ward 001, Iragbiji, yace Oyetola ya samu kuri’u 1,612 inda ya doke sauran yan takara biyu.

Adeoti da Lasun sun ci sifili, 0 a atisayen.

Advertisement

Yace wakilai 2,053 ne aka amince da su don gudanar da aikin, inda yace 1,612 ne suka kada kuri’un su ga gwamnan.

A nasa jawabin, Oyetola ya ce bai yi mamakin samun nasara a unguwar sa ba.

Advertisement