Kasuwanci

Osun: Gobara ta lalata shaguna 12 da kayayyaki a kasuwar Atakumosa

Wata gobara da ta tashi a safiyar ranar Lahadi ta lalata shaguna da kayayyaki na miliyoyin Naira a shahararriyar kasuwar Atakumosa da ke garin Ilesa a jihar Osun.

Rundunar ‘yan kwana-kwana ta jihar Osun da na tarayya sun yi nasarar shawo kan gobarar daga bazuwa, yayin da ‘yan sanda suka hana barayi yin fashi a kasuwar.

Ba a dai gano musabbabin tashin gobarar ba.

Advertisement

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun, Mista Ibrahim Adekunle, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da karfe 2:15 na safe, ta kuma shafi shaguna 12.

Ya ce: “Da misalin karfe 2:15 na safe, an sanar da mu labarin barkewar gobara a shagunan da ke daura da gidan waya a cikin kasuwar Atakunmosa, dandalin Ereja, Ilesa.

“Mun tashi tsaye tare da kashe wutar domin hana ta yaduwa zuwa yankunan da ke kusa.

“A cikin mintuna 30 da isowarmu, mun samu nasarar shawo kan gobarar.

“Duk da haka, shaguna 12 ne gobarar ta yi barna sosai

Advertisement