Al'umma

Ogun: Gwamna Abiodun ya ayyana ‘ƴaki’ kan ƴan Yahoo da masu satar mutane

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya kaddamar da ƴaki da masu damfara ta intanet, wadanda aka fi sani da Yahoo boys.

Domin dakatar da wuce gona da iri da yan damfara ta intanet ke yi a jihar, Abiodun yace nan ba da dadewa ba Ogun za ta kafa hukumarta dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon-kasa domin magance matsalar damfarar yanar gizo da kuma hada-hadar kudade ba bisa ka’ida ba, musamman wadanda ke da alaka da garkuwa da mutane.

Yayin da yake jaddada kudurin sa na kaddamar da yaki da masu garkuwa da mutane, Abiodun ya bayyana cewa gwamnatin sa na hada kai da hukumomin tarayya da takwararta ta jihar Oyo domin tabbatar da tsaron iyakokin.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji suka yi garkuwa da su a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, inda aka biya miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa kafin a sako su.

Domin kawo karshen hakan, Abiodun ya sake kaddamar da rundunar hadin guiwar jami’an tsaron jihar mai suna OP-MESA a ranar Juma’a.

A yayin taron da aka gudanar a filin Arcade, Oke-Mosan, Abeokuta, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta nade hannayenta ba, ta kuma bari a san jihar da dalilan da ba su dace ba.

Kwanakin baya ina wani taro a Abuja, kuma shugaban EFCC ya halarta. Abin bakin ciki, ya ce da ni, Jihar Ogun ce ke kan gaba a jerin ‘Yahoo Yahoo Boys’. A martani na na ce ban yi mamaki ba domin jihar Ogun ce hedikwatar ilimi a kasar nan kuma za ku tarar da irin wadannan cibiyoyin ilimi a kusa da shi kuma ya amince da ni.

Mun yanke shawarar cewa za mu kafa Hukumar Jiha da za a yi niyya don kawar da irin wadannan laifuffuka na kudi. Hukumar mu ta jaha za ta hada kai da hukumar tarayya don kada mu mamaye wancan wurin karya a wannan yanki.

“Muna so mu mamaye na farko a yankuna da yawa, amma ba cikin zamba da Yahoo Yahoo ba.

Da yake magana kan yin garkuwa da mutane a kan hanyar Ogun zuwa Oyo, Abiodun ya bayyana cewa ya tattauna da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo domin su hada kai a fannin samar da tsaro a kan iyakokin jihohin biyu.

Ya kara da cewa Makinde ya kammala shirye-shiryen zuwa Ogun tare da tawagarsa ta jami’an tsaro, domin shirin yadda za’a kamo barayin.

Advertisement