Tsaro

Nijar: Ƴan ta’adda sun kai mummunan hari a jihar Tillaberi

Shaidun gani da ido sun tabbatar da abkuwar harin, inda suka ce da farko dai yan ta’addar sun kwantar da fasinjoji maza ne tare da buɗe masu wuta, a yayinda suka kori mataye da ƙananan yara.

Da yake aika wani saƙo na audio, wani shaidun gani da ido yace : ” yan ta’addar sune suka buɗewa motar wuta, bayan sun kashe maza.

Ya ƙara da cewa : ” babu kowa cikin motar yayinda da ta kama da wuta “

Ya zuwa yanzu dai ana ƙiyasta kusan mutum 19 ne suka mutu a sakamakon wannan mummunan harin na yan ta’adda akan hanyar tera.

Tera birni ne, dake a yankin Tillaberi, a Sashen Tera na Nijar.

Tana da nisan kilomita 175 arewa maso yamma da babban birnin Yamai, kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Advertisement

Kabilar Songhai, Fulani, Gourmantche da Buzu ne suke zaune. Galibin al’ummar manoma ne.

Advertisement