Tsaro

Niger: Yanzu haka yan ta’adda dun kai wa matafiya hari a hanyar Zungeru-Kontogora

Wasu ‘yan ta’adda da aka fi sani da ‘yan bindiga a ranar Talata sun kaddamar da farmaki kan matafiya a unguwar Garun Gabas da ke kan hanyar Zungeru zuwa Kontogora a jihar Neja.

A cewar wani shaidan gani da ido, a halin yanzu matafiya sun makale akan titin Zungeru suna jiran barayin su gama aikin su.

Shaidan gani da ido wanda ya zanta da gidan talabijin na TVC, an ce yana tafiya ne daga Minna zuwa Kontogora.

Advertisement

A halin da ake ciki dai, ‘yan bindigar sun farfasa wata mota da harsasai tare da kwashe fasinjojin da suka mallaka.

Kwanaki hudu da suka wuce, an kashe jami’an ‘yan sanda uku, yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba aka yi garkuwa da su a wani samame da ‘yan bindiga suka kai ofishin ‘yan sanda a jihar Neja.

Advertisement