Tsaro

Niger: Yan bindiga sun kashe DPO Nasko, da wasu mutane shida

Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da kashe wani jami’in yan sanda na DPO da wasu mutane shida a garin Nasko da ke karamar hukumar Magama a jihar a wani kazamin artabu da yan bindiga da suka yi da yan sanda.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar a ranar Talata.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP, Mista Bala Kuryas ya tabbatar da haka a Minna, inda yace an kashe wasu daga cikin yan bindigar, yayin da wasu kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Advertisement

A cewar shi, yan bindigar sun kai farmaki ofishin yan sanda reshen na Nasko a kan babura, kuma an kashe jami’an sashin biyu a yakin da ya biyo baya.

Kuryas ya bayyana cewa, baya ga jami’an tsaro, wasu yan kungiyar yan banga hudu a yankin suma sun rasa rayukan su a yayin musayar wuta da aka yi.

Kwamishinan yace a halin yanzu an aike da tawagar yan sanda da jami’an soji zuwa yankin domin zakulo masu laifin.

Advertisement