Labarai

Netanyahu Zai Shiga Tarihi A Matsayin Mai Kisan Ƙare Dangi – Petro

Gustavo Petro da firaministan Isra’ila na ci gaba da musayar kalaman zazzafan kalamai dangane da yakin Gaza.

Shugaban kasar Colombia, wanda ya buga a kan shafin X, ya ce: “Mista Netanyahu, za ka shiga tarihi a matsayin mai kisan kare dangi. Zuba bama-bamai kan dubban yara da mata da tsofaffi ba zai sanya ka zama jarumi ba.”

Ya kwatanta Netanyahu da ‘yan Nazi da suka kashe miliyoyin Yahudawa a Turai kuma ya ce “kisan kare dangi, kisan kare dangi ne”, ba tare da la’akari da addinin wadanda aka kashe ba.

Tun da farko, Netanyahu ya kira Petro “mai goyon bayan Hamas mai kyamar Yahudawa” bayan da shugaban Colombia ya yi kira da a kame firaministan Isra’ila kan kisan Falasdinawa a Gaza.

Advertisement