Tsaro

NDLEA ta kama wani ɗan kasar Indiya da laifin safarar kwalaben codeine 134,700

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama Vyapak Nutal, wani dan kasuwa dan kasar Indiya, bisa zargin shi da safarar kwalaben maganin codeine guda 134,700 cikin kasar.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Femi Babafemi, kakakin hukumar ta NDLEA, yace wanda ake zargin yayi lodin manyan motoci dauke da maganin a jamhuriyar Benin.

An ce ya shigo ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar ne ya isa Sokoto a Najeriya.

Advertisement

Sanarwar ta ce “Yn zauna a wani otal a jihar Sokoto, bayanan sirri sun nuna cewa Nutal ya fara neman masu siyan maganin,” in ji sanarwar.

“Yayin da jami’an tsaro ke bibiyar shi, jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar sun samu nasarar kama shi tare da mika shi ga NDLEA a ranar Laraba, 10 ga Fabrairu, 2022.”

Kakakin ya kuma ce hukumar ta yi nasarar tarwatsa wani yunkuri na safarar tabar wiwi, methamphetamine, khaat, tramadol da tabar wiwi ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.

A filin jirgin saman Legas, jami’an tsaro a ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu, sun kama Felix Rotimi Eshemokhai da tabar heroin kilogiram 1.75 a lokacin da yake kokarin shiga Royal Air Maroc zuwa Casablanca, Morocco, yayin da wani dan fataken mai suna Okafor Emmanuel Onuzuruike, shi ma an kama shi a wannan rana a yayin yunkurinsa tafiya a kan Rwanda Air zuwa Dubai tare da 2.2kg na tabar wiwi a boye a cikin kayan abinci, “in ji Babafemi.

Kimanin kilogiram 25 na Methamphetamine, Tramadol, Cannabis da Khat da aka boye a cikin sassan mota, na’urar MP3, lasifika da yadudduka masu zuwa Amurka, UK, Australia, Dubai da Madagascar, an kama su a wasu manyan kamfanoni guda uku da ke Legas.

“A jihar Gombe, an kwato capsules guda 31,000 na Tramadol daga wata babbar mota da ta taso daga Onitsha, jihar Anambra, zuwa Mubi, jihar Adamawa da mai shi, Ibrahim Tukur Bage, da aka kama a ranar Juma’a 11 ga watan Fabrairu, a lokacin da yake kokarin tserewa.

Wannan ya biyo bayan kama Aliu Salami, mai shekaru 43, da tabar wiwi kilogiram 143.9 a Oke-Ata, karamar hukumar Abeokuta ta Kudu, jihar Ogun, a ranar Laraba, 9 ga watan Fabrairu.”

Advertisement