Tsaro

NDLEA na neman Abba Kyari ruwa ajallo bisa alaƙa da kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi

Hukumar yaki da sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a ranar Litinin ta bayyana dan sandan nan mataimakin kwamishina, Abba Kyari, da aka dakatar a kwanakin baya wanda take nema ruwa ajallo bisa zargin alaka da kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata gajeriyar ganawa da manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar.

Matakin yazo ne a cikin badakalar Hushpuppi.

Advertisement

Kyari, har zuwa lokacin da hukumar ta dakatar da shi, shine jami’in da ke kula da tawagar da ke ba da bayanai ga hukumar leken asiri ta ‘yan sanda ta Sufeto-Janar.

Tun da farko dai wani rahoto da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ta fitar ya tuhume shi da laifin zamba da ya shafi fitaccen jarumin Instagram, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Advertisement