Al'umma

NCPC ta fara tantance maniyyata aikin hajjin 2021/2022

Hukumar Alhazai ta Najeriya Nigeria Christian Pilgrim Commission (NCPC) ta fara tantance maniyyatan da suka fito daga babban birnin tarayya Abuja don gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2021 da Eastern 2022 zuwa Isra’ila da Masarautar Hashemite ta kasar Jordan.

A cewar sakataren zartaswa na hukumar, Rabaran Yakubu Pam, wannan shine karo na farko da za’a gudanar da gwajin aikin hajjin na shekarar 2021 da kuma shekarar 2022 ta Easter.

“FCT ita ce rukunin farko na maniyyatan da za a tantance su sannan kuma zasu zama na farko da zasu nufi Isra’ila da Jordan a tarihin aikin hajji a Najeriya. Hukumar ta tsara aikin hajjin na bana don ya zama mai tasiri a ruhi da kuma canza sheka ta yadda mahajjata za su dawo su kuma yi tasiri ga rayuwar sauran dake kewaye da su,” inji shi.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga maniyyata da kada su fake da aikin hajji domin tafiyar, kamar yadda ya shawarce su da su kasance jakadu nagari a Najeriya.

Advertisement