Al'umma
Nawa Ne Kuɗin Aikin Hajjin Shekarar 2024 A Najeriya?
A shekarar 2024, hukumar alhazai ta kasa a Najeriya, NAHCON ta tantance mafi karancin kudin ajiya a kan kudi naira miliyan ₦4.5, inda a ka lissafa kudin karshe a kasa da za’a biya daga yankunan kasar.
Kuɗin Yankuna
₦4,899,000 – Kudanci
₦4,699,000 – Arewaci
₦4,679,000 – Yola da Maiduguri
Kudaden aikin Hajji ya yi tashin gwauron zabo daga jiragen sama na kasa da kasa, da masauki, izini (visa), abinci, da makamantansu. Sai dai kungiyar masu gudanar da aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON) ta yi kiyasin cewa farashin zai kai miliyan ₦6, fiye da ninki ₦3 miliyan da mahajjaci daya ya kashe a shekarar 2023.
Duk mun san dalilin da ya sa aka yi hasashen.