Tsaro

NATO ta ce bai kamata yaƙin Rasha ya zarce Ukraine ba

Sakatare-janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya bayyana a jiya talata cewa akwai sahihan rahotanni da ke nuna cewa Rasha na kai hari kan fararen hula a Ukraine, ya kuma bukaci Moscow da ta kawo karshen rikicin, yana mai cewa ba za ta bari ya yadu ba.

Stoltenberg yace “Muna da alhakin da ya rataya a wuyan mu na ganin cewa rikicin bai yi kamari ba kuma ya yadu fiye da Ukraine ba.” “Za mu kare tare da kare kowane inci na dukkan yankunan da ke kawance,” inji shi.

Da yake magana tare da shugaban kasar Latvia Egils Levits, Stoltenberg yace mamayar da Rasha ta yi na haifar da muguwar wahala kuma illar jin kai na da muni.

Advertisement
Advertisement