Siyasa

Najeriya Zata tarwatse idan Jam’iyyar PDP ta fadi zabe a 2023 – Sule Lamido

Sanannen jigo a jam’iyyar PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a kwanakin nan, yayi gargadin cewa Najeriya za ta iya rugujewa idan jam’iyyar PDP ta fadi zabe a 2023, akan haka yayi kira ga jam’iyyar da ta warware matsalolin ta musamman rikicin rabon mukamai.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban jam’iyyar na kasa Dakta Iyiorcha Ayu ya bukaci tsaffin gwamnonin jam’iyyar da su dawo da takwarorinsu da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu, yana mai cewa ‘yan Najeriya na son su dawo jam’iyyar.

Lamido, wanda ya jagoranci wasu tsaffin gwamnonin da suka ziyarci Ayu da mambobin kwamitin ayyuka na kasa, ya bayyana cewa dole ne a fara samun jam’iyya kafin muhawarar akan yankin da Ɗan takara shugaban kasa zaifito.

Advertisement

Ya kara da cewa idan har PDP ta sake samun rashin nasara a 2023, kasarnan za ta iya rugujewa.

Don haka Lamido ya yi kira ga gwamnonin jam’iyyar masu ci da su hada kai da tsaffin gwamnoni domin karfafa jam’iyyar gabanin zaben 2023.

A nasa bangaren, Ayu, wanda ya bayyana jin dadinsa da ziyarar hadin kai da tsoffin gwamnonin suka kai, ya ce sakamakon zaben kansilolin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, ya nuna cewa ‘yan Najeriya na son PDP ta dawo mulki a 2023.

Advertisement