Tsaro

Najeriya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume 15 na ta’addanci a kan Kanu

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume guda 15 na ta’addanci kan shugaban kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, a babbar kotun tarayya dake Abuja.

Advertisement

A ranar Talata ne dai dan gwagwarmayar zai koma kotu domin sauraren shari’ar da ake yi masa na zargin cin amanar kasa.

Tun farko gwamnatin tarayya ta gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhumarsa da laifuka bakwai da suka hada da cin amanar kasa da sauran laifuffuka na hadin gwiwa.

Advertisement

Darakta mai gabatar da kara, M.B. Abubakar, ya sanar da tuhume-tuhume 15 da aka gyara masu lamba FHC/ABJ/CR/383/2015 a ranar Litinin.

An dawo da shugaban kungiyar ta IPOB kasar ne a ranar 27 ga watan Yunin bara.

A farkon watan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da batun sakin Kanu ba tare da wani sharadi ba, ya kuma bukaci ya kare kansa kan tuhumar da ake masa.

Advertisement