Tsaro

Najeriya na shirin mikawa Amurka Abba Kyari akan alaƙa da damfarar miliyan $1.1

Gwamnatin Najeriya ta fara amsa bukatar gwamnatin Amurka ta mika mata DCP Abba Kyari, wani babban jami’in yan sanda. Ana neman mataimakin kwamishina Kyari a Amurka bisa laifin zamba da kuma satar shaida.

Abubakar Malami, babban lauyan gwamnati, kuma ministan shari’a, wanda ya shigar da bukatar mikawa Najeriya takardar neman kasar waje, ya tabbatar wa manema labarai a ranar Alhamis cewa yayi hakan ne bisa bukatar ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.

Ministan yace ya gamsu cewa laifin da ake neman da shi Kyari ba na siyasa ba ne, ko na banza, kuma an gabatar da bukatar a mika shi bisa gaskiya da adalci.

Advertisement
Advertisement