Siyasa

Najeriya Na Bukatar Shugaba Mai Kama-Karya Domin Dai-Daita Lamurra – Sarkin Ilorin

Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya ce Najeriya na bukatar mai mulkin kama karya don dai-daita al’amura a kasar.

Sarkin Sulu-Gambari ya bayyana haka ne a yayin ziyarar wayar da kai da babban bankin Najeriya (CBN) kan sake fasalin kudin Naira da ya kai fadar Sarkin da ke Ilorin ranar Litinin.

Ya ce Najeriya ba ta da shugabanci nagari duk da kimar da kasar ke da ita a duk fadin duniya.

Advertisement

“Nijeriya ta riga ta shiga cikin halin da ake ciki, muna addu’ar kada ta ruguje. An kima mu da kyau a duk faɗin duniya, shugabanci ne kaɗai muka rasa.

“Sai Janar Murtala Mohammed na tsawon watanni shida ya yi wa kasa alheri, bayan haka ba mu taba samun gwamnati irinsa ba.

“Abin da muke bukata shine mai mulkin kama karya don sanya abubuwa a wuri,” in ji sarkin gargajiya na aji na farko.

Advertisement