Kasuwanci

Naira: Bayan Fitar Da Sabbin Kuɗi, CBN Ya Canja Lokacin Da Za’a Daina Karɓar Tsofaffi

Bayan fitar sabbin kuɗi wadanda suka haɗa da ₦200, ₦500 da ₦1000 a yau Laraba, har ila babban bankin na Najeriya, CBN ya sake canja lokacin da za’a daina karbar tsofaffin kuɗi a hukumance.

Kamar yadda shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emiefide ya bayyana a jiya Talata, yace wa’adin kwanaki ɗari sun isa ace duk inda ɗan Najeriya yake ya canja tsofaffin kuɗin shi kafin a rufe karbar su.

Idan ba’a manta ba, a baya an shirya fitar da sabbin kuɗin ne a 15 ga watan Disamba mai kamawa, wanda daga nan za’a cigaba da amfani da sabbin da tsofaffin kuɗin har zuwa 31 ga watan Janairun 2023, lokacin daina amfani da tsofaffin a hukumance.

Bisa ga tsarin farko za’a yi kwanaki akalla 45 kafin rufe karbar tsofaffin, amma saboda canja lokacin fitar sabbin kuɗin, daga yanzu akwai kimanin akalla kwanaki 80 ga duk mai tsofaffin kuɗin ya canja su kafin wannan lokacin.

Advertisement