Al'umma
Nadia Nadim: Yarinyar da ƴan Taliban suka kashe mahaifinta tana ƴar shekara 11

Ƴan Taliban sun kashe mahaifin Nadia Nadim tun tana karama. Ta tsere daga Afghanistan, a cikin wata babbar mota, tana da shekara 11, daga karshe ta isa ƙasar Denmark.
Yanzu ta zura kwallaye 200 a raga, kuma ta wakilci tawagar kasar Denmark sau 99. Nadia na magana da harsuna 11 na duniya, sannan kuma yana cikin jerin Forbes na Mata masu ƙarfi a wasannin duniya.
A wannan makon, ta cancanci zama likita bayan shekaru 5 tana karatu a lokacin da take buga kwallon kafa.
Abin koyi ga kowa da kowa! 🇦🇫❤️🇩🇰