Taskar Labarai
Trending

Naci Kudin Wani Dan China Na Kasa Bacci Kubani Shawara Kar Yazo Ya Kashe Ni Nima Cewar Wata Budurwa

A makon jiya ne wani dan kasar China ya je har cikin gida ya halaka budurwarsa ‘yar Kano mai suna Ummita a unguwar Janbulo da ke jihar Kano.

Wannan al’amari ya firgita wata budurwa wacce itama tana da saurayi dan kasar waje, a yanzu haka ta rasa sukuni.

A cikin wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, budurwar ta koka cewa ta kasa bacci tun bayan da ta samu labarin kashe Ummita da dan Chinan yayi.

Budurwar wacce ke neman shawarar jama’a, tace ko shakka babu taci kudin mutumin sosai kuma yanzu ta rasa yaya zata yi.

Ta ce:

“Jama’a, bacci nake so nayi na kasa. Hmmm wani abu ne yake bala’in damuna, dan Allah ku bani shawara. Soyayya nake yi da wani dan kasar waje, bana so in fadi kasar, kuma har ga Allah naci kudinshi, naci kudinshi, naci kudinshi. Abun da ya faru da Ummita ya tsaya mun a rai, yanzu ni yaya zanyi? Ku bani shawara.
“Na shiga uku, innalillahi wa’inna illaihi raji’un, dan Allah kada ku dauki abun nan wasa, jama’a ku bani shawara.”

Jama’a sun yi martani
fulata_mahre ya ce:

“Naakulle da makulli kaff .”
bin_saleehu ya yi martani:

“Ko kudinsa ko aurensa tunda ba damu kika ci kudinba mayaudariyya.”

itx_reality ya ce:

“Kunfi kusa .”
mairodahiru20 ta ce:

“Gani ga wane dai.”
b______________black ya ce:

“Too ki aure shi mana ko ki biya shi kudin sa ko ki yarda yayi abunda zai dake na kudin sa ‍♂️Tunda ku mayun kudi ne.”
ramlah_collection_7886 ta ce:

“In kina sonshi ki aure Shi in ya yarda zai karbi muslinci ko ki nemeshi kibashi kudinshi kuyi sulhu”

Back to top button