Al'umma

Na So In Sayar Da Budurwa Ta Da Dan-ta, Don Ta Ci Amana Ta

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wasu ‘yan uwa biyu, Ayomide Babtunde da Gbenga Babatunde bisa zargin su da yin garkuwa da wata mata da dan-ta domin yin tsafi. Lamarin wanda kakakin rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da cewa, ‘yan sandan jihar Ogun sun kama ‘yan’uwan biyu a safiyar ranar 30 ga watan Disamba, 2022.

Advertisement

Babban wanda ake zargin wanda babban yaya ne, Ayomide Babatunde ya yi niyyar sayar da budurwar shi da dan-ta. Wanda ake zaton mai saye wanda aka bayyana a matsayin Jacob Olorunto ya amince ya sayi mutanen biyu. Duk da haka, yana da shirin kai rahoto ga ‘yan sanda. Da tsakar dare a gidan Jacob Olorunto, wasu matasa ‘yan kabilar Igbo Obe sun kutsa cikin gidan tare da damke mutanen biyu tare da hadin gwiwar ‘yan sanda.

Babban yayan wanda shine babban wanda ake zargin ya yi zargin cewa ya so ya sayar da budurwar ne saboda ta fara lalata da wani mutum. Ya ce, ”Na hadu da budurwa ta kimanin watannin baya. Mun shaku sosai, ita kuma ta so mu yi aure. Amma bana son auren ta domin ta riga ta haifi ɗa. A gaskiya ban sani ba ko ta ga niyya ta, amma na gano cewa ta fara yaudara ta. Ba na son in rasa ta ga wani mutum sai na kira kani na na ce mai ya nemo yadda za mu sayar da ita da dan-ta.

Advertisement

Yaya na ya samu tuntubar wani baba wanda yake son siyan su biyu akan kudi N600,000. Don haka sai na lallabi budurwa ta, ta biyo ni gidan mai siya, na ce mata za mu je gidan uba na mu yi sabuwar shekara. Muka isa gidan baban da yake son siya mata da dan ya kyauta ta mana. Amma na lura ya rika fita yana shigowa, da misalin karfe 11:00 na dare wasu samari suka shiga gidan suka kwace dukkan wayoyin mu, suka kai mu ofishin ‘yan sanda.

Advertisement