Al'umma

Na kwanta da ɗana don in samarwa mijina ɗa – Inji wata Uwa

Matina da mijinta na biyu James

Wata uwa ta yi ikirarin cewa ta yi lalata da danta na haihuwa domin kawai ta haifi jariri ga mijinta.

Matina Agawua yar asalin garin Yelwata a jihar Nasarawa ta rasa mijinta na farko sakamakon harin da makiyaya suka kai wa a Arewacin Najeriya. Auren ta na farko ta haifi ɗa.

Ta sake yin aure shekaru da yawa bayan mutuwar mijinta amma ta sami matsala bata haihu ba tare da mijinta na biyu Mista James ba.

Advertisement

Bayan shekara shida da yin aure ba tare da haihuwa ba, Matina ta fara samun matsuwa daga surukar ta da mijinta na yanzu cewa ta haifi ɗa ko kuma auren ya mutu.

Mijin Matina ya yi barazanar cewa zai auri sabuwar mata kuma hakan ya dami Matina domin ita da mijinta sun ba da gudummawar kuɗi don gina gidan da suke zaune, inda Matina ta ba da kaso mai yawa.

Lamarin rashin haihuwar da kuma batun kawo wata mace ta zauna da mijinta na biyu a gidan da ta gina tare da mijin ya dame ta.

A sakamakon haka, Matina ta yanke shawarar yin lalata da ɗanta matashi tun farkon auren ta don ganin ko za ta iya haifa wa mijinta na biyu ɗa.

Advertisement