Al'umma

“Na kashe Hanifa da gubar bera, na binne gawarta” – Inji Mal. Abdulmalik

HOTO: Abdulmalik Muhammad Sambo, wanda ya kashe Hanifa Abubakar.

A kwanakin baya ne rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ya kashe yar shekara 5, Hanifa Abubakar, wanda yayi kisan mai suna Abdulmalik Muhammad Sambo ya shaidawa yan sanda yadda ya kashe karamar yarinya, Hanifa.

Yayin da yake magana a wani faifan bidiyo da yan sanda suka fitar a jihar Kano, wanda yayi kisan Abdulmalik Muhammad Sambo yace: “Ni malamin makarantarta ne, na shirya sace ta a karon farko amma abin ya ci tura, na je makarantar da kaina na yi garkuwa da ita. Hanifa ta kai mako biyu a gidana tare da matata da ya’ya na.

Abdulmalik ya kara da cewa: “Lokacin da wasu malaman makarantarmu suka kawo min ziyara, na dauka sun san cewa na sace Yarinyar ne, shi ya sa na ba ta Gubar bera, nan take ta mutu, na sa gawarta a cikin jaka na binne ta a cikin harabar makarantar don gudun tuhuma.

Advertisement

Haka dai wanda ya kashe Hanifa ya shaidawa rundunar yan sandan jihar Kano bayan an kama shi.

Advertisement