Siyasa

Na Goyi Bayan Atiku A 2019, Amma Bayan Ya Samu Tikitin Takara Sai Ya Daina Ɗaukar Waya Ta – Jonathan

Idan za’a iya tunawa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 tare da Ifeanyi Okowa, abokin takarar shi, sun ziyarci Jonathan a gidan shi da ke Abuja a daren ranar 17 ga watan Nuwamba, a kan “aikin zaman lafiya” biyo bayan halin ko-in-kula da yayi a rikicin PDP da yakin neman zaben shugaban kasa baki daya.

Wasu majiyoyi da suka san taron na daren Alhamis sun bayyanawa jaridar TheCable cewa Atiku ya shaidawa Jonathan cewa ya damu cewa tsohon shugaban kasar baya shiga harkokin jam’iyyar PDP yayin da zaben shugaban kasa ke kara kusantowa.

Ya roki Jonathan da yasa baki a rikicin da ke tsakanin ahi da gwamnonin PDP da ke goyon bayan Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, inji majiyar.

Majiyoyi sun shaida wa TheCable cewa Jonathan yayi amanna cewa jam’iyyar musamman Atiku ba ta nuna masa wani girmamawa ba.

“Ba a taba gayyatar Dr Jonathan zuwa taron kwamitin amintattu ba,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

“Jam’iyyar ba ta taba ba shi daraja ta sanya shi cikin ayyukan ta ba. Yanzu da zaben shugaban kasa ya kusa, ba zato ba tsammani Dr Jonathan ya zama muhimmi.”

Rahotanni sun bayyana cewa Jonathan ya tunatar da Atiku cewa ya mara masa baya sosai a takarar shi ta shugaban kasa a 2019 amma dan takarar ya daina karbar kiran shi bayan samun tikitin takara.

“Bugu da kari kuma, ba a nada wadanda Dr Jonathan ya zaba a majalisar yakin neman zaben shugaban kasa a 2019 ba. Ba a zabo ko daya daga cikin wadanda aka nada nasa ba,” majiyar ta kara da cewa.

Advertisement