Laifuku

Na Bai Wa Ummukhulsum Miliyan ₦90 Domin Sayen Gida Da Kasuwanci – Inji Ɗan Chinar Da Ya Kashe Budurwar Shi Ƴar Kano

Dan kasar China da ya kashe wata mata ƴar Kano Ummakulsum

A ranar Juma’a ne babbar kotun Kano ta saurari wasu kalamai da wani dan kasar China mai suna Frank Geng-Quangrong ya rubuta, wanda ake zargin ya kashe wata mazauniyar jihar Kano, kuma budurwar shi Ummukulsum Sani.

A cigaba da sauraren karar a gaban mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, Mista Quangrong ya amsa cewa ya yiwa Ummukhulsum tsatsauran hukunci ne bayan da ya fusata da kai masa hari sa suka yi.

A cikin kalaman da ya mika wa ‘yan sanda, Quangrong wanda ya musanta cewa yayi niyar kashe Ummukhulsum, yace dole ne ya mayar da martani a matsayin ramuwar gayya daga marigayiyar da iyalan ta baki daya.

Jawaban sun fito ne daga bakin Insifeto Ijuptil Mbambu, jami’in bincike na sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID) a gaban kotu.

A wasu kalamai da Quangrong ya fitar, yayi ikirarin cewa ya saka Naira miliyan ₦80 a asusun Ummukhulsum don kafa kasuwanci, gina gida da sauran kayayyakin masarufi.

A cewar ɗan kasar Sin ɗin, Ummukhulsum ta yi tafiya tare da wani mutum a watan Maris 2022 zuwa Abuja. Yace bayan wata biyu sai ta dawo Kano suka koma da alakar su.

“An bar ni cikin ruwan sama na tsawon sa’o’i da dama don ganin Ummukulsum a wannan dare ina kwankwasa kofa. Iyalin sun ki bude kofa. A daidai lokacin, daya daga cikin yayan Ummukulsum ya zo ya bude kofa amma ya hana ni shiga sai ya karbi kare da na kawo, inji shi.

“Daga baya aka bar ni na shiga dakin da Ummukulsum take zaune domin tattaunawa da ita. A lokacin da na shiga dakin, na fuskanci gaba dayan ’yan uwa suna ta kai mani hari tare da yi mini rauni a wuya da hannaye na. A lokacin ne na fito da wuka ta da nake amfani da ita don kare kai, na cakawa Ummukulsum sau biyu a kafadar ta.

“Kafin wannan lokacin, na saka Naira miliyan ₦60 a asusun Ummukulsum na GTBank don zuba jari, Naira miliyan ₦8 na karatun ta a Sakkwato, Naira miliyan ₦4 don siyan gida da kuma Naira miliyan ₦18 don kasuwanci. Amma da na ziyarci Ummukulsum na gane cewa babu kasuwanci kuma babu mota,” in ji jawaban ɗan ƙasar Sin ɗin.

Mai shari’a Ma’aji ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 19, 20 da 21 ga Disamba, 2022 domin cigaba da sauraren karar.

Advertisement