Al'umma

N250m: Muna da marayu da dama a Arewacin Najeriya – Kungiyar ta shaida wa Davido

N250m: Muna da marayu da dama a Arewacin Najeriya – Kungiyar ta shaida wa Davido

Wata kungiya mai suna Support Group for Nigerian Orphans (AGNO) ta yi kira ga mawakin nan da ya lashe kyautar waƙoki David Adeleke wanda aka fi sani da Davido da ya dauki marayu a yankin Arewacin kasar nan tare da raba Naira miliyan 250 ga gidajen marayu.

Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta Salisu Waziri Ibrahim ta yi wannan kiran a ranar Lahadin da ta gabata a Jalingo babban birnin jihar Taraba, inda yace kara kaimi ga gidajen marayun na arewa zai taimaka matuka wajen magance dimbin kalubalen da suke fuskanta.

Kungiyar ta ce ya zama dole su tunatar da Davido tushen sa.
Davido, in ji shi, an haife shi a arewa, amma da wuya ya ziyarci kuma ba ya da alaka da wasu abubuwa.

Sun ce, “muna da marayu da dama a wannan yanki na kasar nan, wadanda ba za su iya daga murya ba sai dai idan wasu daga cikin mu kungiyoyi masu zaman kansu da ke yi musu magana” sun jaddada cewa “da yawa daga cikinsu sun kasance a sansanoni.”

Ku tuna cewa Davido yace Naira miliyan 250 da ya karba daga magoya baya, abokai da iyalai za a ba da gudummawar ga gidajen marayu da ke baje a fadin Najeriya.

Back to top button