Al'umma

Mutumin da ya saci keken Napep, ya sayar da shi kan ₦23,000 a Ogun

An kama wani mai suna Azeez Saka da laifin satar babur mai kafa uku, wanda aka fi sani da Keke Napep a garin Alagbado dake kan iyaka tsakanin jihohin Legas da Ogun.

Advertisement

Jami’an tsaro mallakar gwamnatin jihar Ogun, So-Safe Corps ne suka kama Saka.

An kama shi ne tare da wasu mutane biyu, Abdulkadri Dauda da Uthman Hudu, wadanda aka ce sun sayar da babur din da ya sato a kan kudi ₦23,000.

Advertisement

A cewar wata sanarwa da kwamandan So-Safe Corps na jihar, Soji Ganzallo ya fitar, wani mai korafin ya kai rahoton bacewar babur mai lamba LSR602QG a ofishin ‘yan sanda na Alagbado, inda ya ce an kuma tuntubi So-Safe don tabbatar da gano babur din kama masu laifin.

Advertisement