Al'umma

Mutane Sun Yiwa Sanusi Lamido Barka Da Zuwa Bukin Mauludi A Landan

Jama’a da dama ne suka tarbi tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a wajen bikin Mauludi da ake gudanarwa duk shekara a birnin Landan. Sarki Sanusi Lamido da Jami’an tsaronsa sun halarci bikin a matsayin manyan baki.

Advertisement

Shahararriyar kungiyar Musulunci a birnin Landan, (Ahlul Faida) ta shirya Mauludin na musamman tare da gayyatar daya daga cikin shugabannin Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sarki Sanusi Lamido Sanusi a matsayin babban bakonsu na musamman.

Kalli wasu hotuna da aka dauka a lokacin bikin Mauludi na shekara a Landan a kasa.

Advertisement

Haƙiƙa, an san Mauludi a matsayin bukin Maulidin Annabi Muhammadu. Ana iya samun nau’o’in ibada daban-daban da suka shafi mauludin Annabi Muhammadu a lokacin rayuwar Annabi Muhammadu da kansa, karkashin halifancin Umar, da kuma karkashin dauloli daban-daban na farko na Musulmi kamar Abbasiyawa, Zengids da Fatimidu.

Haka kuma, Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya dauki bikin Mauludi a matsayin wani lamari na wajibi a Musulunci.

Advertisement