Al'umma

Mutane fiye 60 sun mutu a wani hatsarin jirgin kasa a DR Congo

Wani hatsarin jirgin kasa a kudu maso gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 60, kamar yadda kamfanin jiragen kasa na kasar da majiyoyin kasar suka sanar.

“A halin yanzu, adadin wadanda suka mutu ya kai 61, maza, mata da yara, mutane 52 suka jikkata wadanda aka kwashe,” Marc Manyonga Ndambo, darektan samar da ababen more rayuwa a kamfanin jirgin kasa na SNCC, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Asabar.

Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito gwamnan lardin Fifi Masuka na cewa mutane 60 ne aka kashe.

Advertisement

Wani jirgin dakon kaya ne wanda ke dauke da “hanyoyi dari da dama”, in ji Manonga.

Ya kara da cewa “har yanzu wasu gawarwakin na makale a cikin motocin da suka fada cikin kwazazzabai.”

Advertisement