Tsaro

Mutane da dama sun jikkata bayan tashin bam a wata kasuwa mai cunkoso a Congo

Akalla mutane hudu ne sun jikkata bayan fashewar wani bam a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a gabashin birnin Beni na Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a ranar Asabar.

Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki kadan bayan ofishin jakadancin Amurka da ke Kinshasa babban birnin kasar ya yi gargadin kai hari.

Yan sandan yankin sun ce suna neman wanda ake zargin ya tayar da bam ne bayan tashin bam a yankin gabashin kasar inda dakarun Congo da Uganda suka kaddamar da yaki da wasu da ake zargin ‘yan tawaye dauke da makamai.

Advertisement

Kakakin ‘yan sandan birnin Beni Nasson Murara ya ce “Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu.”

Yan sanda sun yi ta fama da masu raunuka a kasuwar kafin a kai su asibitin yan sanda, inji wani dan jaridan kamfanin dillancin labarai na Reuters da ke wurin.

Advertisement