Al'umma

Mutane 56 sun mutu a wani harin bam da aka kai wani masallaci a Pakistan

Wani jami’in asibiti yace adadin wadanda suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a masallacin ƴan Shi’a a birnin Peshawar dake arewa maso yammacin Pakistan ya karu zuwa 56.

Asibitin karatu na Lady Reading, inda aka kawo mafi akasarin wadanda harin bam din na ranar Juma’a ya rutsa da su, yace a cikin wata sanarwa da aka fitar an kawo mutane 194 da suka samu raunuka.

Shugaban yan sandan Peshawar Muhammed Ejaz Khan yace rikicin ya fara ne lokacin da wasu mahara biyu dauke da makamai suka bude wuta kan yan sanda a wajen masallacin. An kashe maharin daya da dan sanda daya a arangamar da aka yi da su, sannan wani jami’in dan sanda ya samu rauni. Wanda ya rage a cikin masallacin kuma ya tayar da bam.

Advertisement

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma duka kungiyar ISIS da kungiyar Taliban ta Pakistan sun kai irin wannan hare-hare a yankin da ke kusa da kan iyaka da kasar Afganistan.

Shayan Haider, wanda ya shaida, yana cikin shirin shiga masallacin, sai wata fashewa mai karfi ta jefa shi kan titi.

Advertisement