Al'umma

Mutane 5 sun mutu a lokacin da suke aikin hako yashi a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane 5 da suka makale a karkashin tulin yashi a kauyen Yanlami dake karamar hukumar Bichi.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ga manema labarai ranar Lahadi a Kano, tace lamarin ya faru ne da safiyar Asabar.

“Mun samu kira daga tashar kashe gobara ta Bichi cewa ramin tafkin ya rufe mutane 5. Mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:05 na safe,” inji Abdullahi.

Advertisement

Ya bayyana sunayen wadanda abin ya shafa kamar haka Alasan Abdulhamid, dan shekara 22,  Jafaru Abdulwahabu, 30, Jibrin Musa, 30, Masaudu Nasiru, 25, Muhammad Sulaiman, 35.

“Wadanda abin ya rutsa da su sun makale ne a lokacin da suke aiki a wani ramin kududdufi domin su samu yashi da nufin su taimaka wa abokinsu da zai yi aure ya gina gida. Wani bangare na yashi ya rufta ya rufe su kuma suka mutu daga baya,” Abdullahi ya ce a cikin sanarwar.

Advertisement