Kasuwanci

Mutane 4,500 sun rasa aikin yi, yayin kamfanin KPMG ya fice daga Rasha da Belarus

Wani kamfani mai kula da lissafin kudi na kasa da kasa, KPMG ya sanar da matakin da ya dauka na yin watsi da mambobin shi a Rasha da Belarus saboda cigaba da mamayar da sojojin Rasha ke yi a kasar Ukraine.

KPMG ya bayyana cewa kamfanonin shi a Rasha da Belarus suna da kusan ma’aikata 4,500, wadanda hukuncin ya bar su cikin wani yanayi.

Kamfanin ya sanar da hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake yin rajistar rashin amincewar shi da mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine, inda Majalisar Dinkin Duniya tace an kashe sama da fararen hula 700.

Advertisement

KPMG ta wallafa a shafin shi na Twitter da aka tabbatar: “Mun yi imanin cewa muna da alhakin, tare da sauran kasuwancin duniya, don mayar da martani ga cigaba da harin da sojojin gwamnatin Rasha ke kaiwa Ukraine, sakamakon haka, kamfanonin mu na Rasha da Belarus za su bar cibiyar sadarwar KPMG.

Advertisement