Kasuwanci

Mutane 18 sun mutu sakamakon ruftawar ƙasa a wata zinare a Guinea

Akalla mutane 18 ne suka mutu sakamakon ruftawar wata mahakar zinari a yammacin kasar Guinea, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar ta bayyana.

A cewar Ousmane Gaoual Diallo wanda ya zanta da manema labarai a ranar Alhamis, hatsarin ya afku ne a ranar Litinin a Gaoual mai tazarar kilomita 386 daga Conakry babban birnin kasar. A cikin yan watannin nan, masu hakar ma’adinai sun yi tururuwa zuwa wurin don neman zinare.

“A halin yanzu, an ciro gawarwaki 18 kuma ba mu gama ba tukuna. Ana cigaba da ayyukan ceto,” Diallo ya fadawa manema labarai.

Advertisement

Hatsari na zama ruwan dare a wuraren da ake kira ma’adinan sana’o’in hannu a fadin Afirka ta Yamma, wadanda ke aiki ba tare da sanya ido ko ka’ida ba.

A watan Mayun da ya gabata, an kashe akalla mutane 15 a wani irin wannan lamari a wata ma’adanin zinari da ke yankin arewa maso gabashin Siguiri. Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 17 ne kuma aka kashe a wata zabtarewar kasa a watan Fabrairun 2019 da wasu dozin tara bayan haka.

Advertisement