Al'umma

Mutane 18, Shanu 16 Sun Mutu A Wani Hatsari Kan Hanyar Sokoto Da Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 18, da shanu 16 a lokacin da wata babbar mota da ke jigilar fasinjoji da shanu ta yi hatsari a kauyen Malisa da ke karamar hukumar Gwandu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi ranar Litinin. Ya ce hatsarin ya afku ne a ranar Lahadi da misalin karfe 11:00 na dare. lokacin da direban motar ya rasa iko da motar a kauyen Malisa da ke kan titin Aliero zuwa Sokoto.

Mista Abubakar ya ce motar mai lamba SRP 442 XA tana jigilar fasinjoji da shanu daga karamar hukumar Illela ta jihar Sokoto zuwa Legas.

Advertisement

“Da isa mahadar Malisa, direban ya rasa iko da motar, sai ta fadi. Sakamakon haka, fasinjoji 42 sun samu raunuka daban-daban. Bayan samun rahoton, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Magaji-Kontagora, ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kwashe wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gwandu domin yi musu magani,” sanarwar ta bayyana.

“Wani likita a asibitin ya tabbatar da mutuwar mutane 18, yayin da sauran wadanda abin ya shafa ke karbar magani a halin yanzu. Hakazalika, shanu 16 su ma sun mutu sakamakon hatsarin,” Mista Abubakar.

Advertisement