Al'umma

Mutane 17 sun kone kurmus bayan wata tankar mai ta yi bindiga a Ogun

Akalla mutane 17 ne aka tabbatar da mutuwar su a wata fashewar wata tankar mai dake kan hanyar Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta tabbatar da cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Juma’a, a unguwar Isara dake kan babbar hanyar.

Mai magana da yawun hukumar FRSC a Ogun, Florence Okpe, ta ce an gano gawarwaki 17 a gobarar, yayin da 14 daga cikin gawarwakin suka kone yadda ba’a iya gane su ba.

Advertisement

“Ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, amma an gano gawarwakin mutane 17.

“An gano Ome namiji, mace daya, da kuma yaro mace daya, yayin da wasu suka kone ba a iya gane su ba kuma babu wani rauni da ya samu,” Okpe ya bayyana.

Ta bayyana cewa motar dakon mai ta yi karo da wata motar bas Mazda mai lamba ZT728 KLD. Ta bayyana cewa kuma abubuwan da ake zargin su ne suka haddasa hatsarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane, sun hada da keta dokar hanya da tukin mota mai hatsari, na ganganci.

A halin da ake ciki kuma, Kwamandan hukumar FRSC reshen Ogun, Ahmed Umar ya koka da cewa za’a iya kaucewa hadarin idan aka bi ka’idojin tuƙi.

Umar ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma umurce su da su tuntubi ofishin FRSC da ke Ogere domin samun karin bayani game da hadarin.

Advertisement