Ƙetare

Mutane 14 Sun Mutu, Wasu Da Dama Sun Ɓata Yayin Da Ambaliyar Ruwa Ta Share Masu Ibada

Akalla mutane 14 ne aka tabbatar da mutuwar su yayin da wasu da ba a tantance adadin su ba suka bace bayan wata ambaliyar ruwa da ta tashi daga kogin Jukskei da ke birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, ta lakume masu ibada a yayin wani biki a wani coci, kamar yadda jami’an ceto suka bayyana a ranar Lahadi.

Kakakin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta birnin Johannesburg wanda ke gudanar da ayyukan bincike da ceto, Robert Mulaudzi, ya ce gungun masu ibada 33 ne suka shiga ibadar coci a gabar kogin lokacin da ambaliyar ta afku a ranar Asabar.

“Wasu daga cikin jama’a sama da 30 ne ke tsaye a kan duwatsu a cikin kogin domin gudanar da ibada a ranar Asabar, lokacin da kogin ruwa ya mamaye,” in ji shi a wani taron manema labarai.

Advertisement

Ya kara da cewa “Faston ya sami ceto ne bayan da ya makale a wani reshen bishiya mai tsawo yayin da ruwan ke dauke da shi.”

“Da farko mun gano gawarwaki tara kamar ranar Asabar amma a ranar Lahadi, mun sake gano wasu gawarwaki biyar, wanda ya kai 14 da suka mutu.

Advertisement