Mutane 12 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara

Akalla mutane 12 ne aka tabbatar da tafiyar su lahira a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Ilorin zuwa Ogbomoso a ranar Asabar.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatarwa manema labarai faruwar hatsarin a Ilorin.
Yace hatsarin ya afku ne a unguwar Ote kuma ya hada da wata farar motar kirar Toyota Hummer wacce ba ta da lambar rajista ba da kuma motar Volvo.
Jami’in FRSC ya dora alhakin faruwar hatsarin a kan saba ka’idojin zirga-zirga.
Ya ce hatsarin ya afku ne a unguwar Ote kuma ya hada da wata farar motar kirar Toyota Hummer ba tare da lambar rajista ba da kuma motar Volvo.
Jami’in FRSC ya dora alhakin faruwar hatsarin a kan saba ka’idojin zirga-zirga.
Ya ce mutane 18 ne suka yi hatsarin inda aka tabbatar da mutuwar mutane 12 yayin da wasu shida suka jikkata.