Kasuwanci

Mutane 109 da suka yi nasara a gasar ‘Glo Joy Unlimited Extravaganza’

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka samu karin ma’abota layin Glo 109 a Abuja sun karbi kayayyaki daban-daban da suka samu a gasar Joy Unlimited Extravaganza.

Kayan sun haɗa da sabuwar Kia Rio, mutane 32 suka lashe firij, 38 da suka lashe na’urorin talabijin da kuzma wasu da suka lashe injunan a wutar lantarki 38.

Manajan Jiha na Globacom, Ibrahim Katsina, yace da aka yi taron gabatarwa a Abuja, za a kammala gabatar da kyaututtukan tare da bikin bayar da kyaututtuka na karshe da za’a yi a Victoria Island, Legas, ranar Alhamis mai zuwa, 27 ga Janairu.

Advertisement
Advertisement