Ra'ayoyi

Musulman Arewa 2 da zasu iya zama mataimakan Osinbajo idan ya fito takara a 2023

Har yanzu dai ba sabon labari ba ne cewa wasu yan takarar shugaban kasa, sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa, a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress APC, a 2023.

Daga cikin yan takarar shugaban kasa, wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa, akwai gwamnan jihar Kogi, Gwamna Yahaya Bello, da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gwamna David Umahi gwamnan jihar Ebonyi da dai sauransu.

Sai dai har yanzu wasu yan takarar ba su bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa ba amma akwai alamun cewa, za su iya tsayawa takarar shugabancin kasar. Daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da ka iya tsayawa takarar shugaban kasa akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Alamu sun nuna cewa Osinbajo na iya tsayawa takarar Shugaban kasa a APC. Duk da cewa bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa ba, ga Jama’a amma masu goyon bayansa sun yi ta kaiwa ga fitattun yan Najeriya game da burinsa na Shugaban kasa.

Duk da haka, Osinbajo yana bukatar amintaccen Mataimaki na Musulmi daga Arewa, wanda zai iya yin takara tare da shi a 2023. Daya daga cikin amintattun Musulmin Arewa da za su iya yin takara da Osinbajo a 2023 shi ne Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.

Farfesa Zulum Musulmin Arewa ne mai suna a jiharsa. Ko shakka babu idan har za a iya zabar Gwamna Zulum a matsayin mataimakin Osinbajo, takarar shugaban kasa a 2023 zai zama mai sauki ga APC.

Idan dai ba a manta ba, an yi ta rade-radin cewa Gwamna Zulum za a hada shi da Farfesa Yemi Osinbajo, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar Shugaban kasa.

Hakan na nufin idan aka zabi Gwamna Zulum a matsayin mataimakin shugaban kasa Osinbajo, APC za ta samu sauki sosai wajen lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Wani Musulmin Arewa da zai iya takara da Osinbajo, shi ne Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai. el-Rufai ya taka rawar gani sosai, a matsayinsa na Gwamnan Jihar sa.

Idan dai ba a manta ba an sha ta yada jita-jita da batanci da Jama’a ke yi cewa za a zabi Gwamna el-Rufai, a matsayin abokin takarar Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023.

Duk da cewa Gwamna el-Rufai bai fito fili ya bayyana tsayawa takarar Mataimakin Shugaban kasa ba amma yana daya daga cikin ’yan takarar da suka fi cancanta a Arewa, wanda ya fi dacewa da Mataimakin Shugaban Kasa, tare da Farfesa Yemi Osinbajo.

Kasancewarsa Kirista, Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yana bukatar Kiristan Arewa ya tsaya takara tare da shi a 2023, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar Shugaban kasa.

Advertisement